Makarantar marayu da marasa galihu na gidauniyar Rochas ta dauki dalibai 200 a Zariya

Makarantar marayu da marasa galihu na gidauniyar Rochas ta dauki dalibai 200 a Zariya

Makarantar marayu da marasa galihu na gidauniyar Rochas ta fara zangon karatu na farko da dalibai 200 a Zariya daga cikin kimanin 4,000 da suka nemi shiga makarantar.

Makarar marayu da marasa galihu da ke Zariya wanda gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya kafa wato ‘Rochas Foundation’ ta fara zango karatu na farko da dalibai dari biyu wanda ta hada da mata da maza a matsuguninta na dindindin wanda ke kan hanyar Kaduna zuwa Kano a garin Zariya.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa, Hajiya Rabiatu Ibrahim wanda ita ce shugabar kwalejin ta sanar da wannan labari a yayin da take zantawa da manema labarai a ranar Talata da ta wuce a garin Zariya.

Hajiya Rabi’atu ta bayyana cewa kwalejin ta fara koyarwa da kimanin dalibai dari biyu wadanda sun kasance marayu da marasa galihu a matakin farko na karamar sakandare, wato JSS 1.

Makarantar marayu da marasa galihu na gidauniyar Rochas ta dauki dalibai 200 a Zariya
Dalibai na makarar marayu da marasa galihu da ke Zariya

Ta ci gaba da cewahukumar makarantar ta rabawa daliban kayan karatu kyauta, wanda suka hada da littattafai da tufafi da takalma da kuma samar musu da abincin rana a kowace rana.

KU KARANTA:Kotu ta jefa wani mutum gidan kaso da laifin neman matar aure

Shugabar ta jaddada cewa makarantar ta yi kudirin baiwa daliban ingantaccen ilimi game da tarbiya yadda daliban za su iya gwagwarmaya da sauran dalibai a fadin kasar.

Hajiya Rabiatu ta kuma sanar cewa sun fara gudanar da karatu ne a karkashin gidauniyar Rochas Foundation College a Adamawa ,Bauchi ,Sakkwato da sauran jihohin arewa.

A jawabinsa, mai kula da kwalejin shiyar zariya, kuma mataimakin shugabar kwalejin, Mista Okpo Kenechuku, ya bayyana cewa kimanin dalibai dubu hudu ne suka nemi shiga makarantar.

Mista Kenechuku ya nema hadin kai masu ruwa da tsaki a yankin da su ba su goyon baya don ci gaban kwalejin.

Ya kuma nemi goyon bayan gwamnatin jihar don samar wa dalibai hanyoyin sufuri wanda zai tamaka musu wajen zuwa da komawa a yayin karatunsu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel