Barayin gwamnati ke sukar Buhari kan kashe-kashen Binuwai - inji Garba Shehu

Barayin gwamnati ke sukar Buhari kan kashe-kashen Binuwai - inji Garba Shehu

- Garba Shehu yace masu tsegumi kan kashe-kashe barayi ne

- An tafka kashe-kashe a Binuwai da Taraba

- Malam Garba Shehu hadimi ne ga Atiuku a da

Barayin gwamnati ke sukar Buhari kan kashe-kashen Binuwai - inji Garba Shehu
Barayin gwamnati ke sukar Buhari kan kashe-kashen Binuwai - inji Garba Shehu

Garba Shehu, Hadimi ga Shugaba Buhari kuma tsohon hadimi ga Atiku Abubakar, yace duk masu gutsuri tsoma kan shugaba Buhari bai dauki matakin gaggawa a Binuwai ba barayi ne da ke neman laqa wa shugaban kashin-kaji

A hirarsa da jaridar Punch, Garba Shehu ya ce gwamnati tana bakin kokarinta kan wannan lamari, kuma ana shawo kan matsalar.

Shugaba Buhari ma dai ya kare kansa a walima da ya hada a daren shekaranjiya inda ya ce yana sane da duk me yake faruwa, amma sai ya dauki lokaci sannan yake daukar mataki, saboda ya sami lokacin tunani da fahimtar me yake faruwa.

DUBA WANNAN: Buhari bai gayyaci Tinubu ba a dinar jiya, me yayi zafi?

Malam Garba Shehu kuwa, yace wadanda suke ta sukar shugaba Buharin kan dadewarsa bai dauki mataki ba, dama barayi ne masu kokarin sai gwamnatin ta kife domin su guji sharia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng