Kotu ta jefa wani mutum gidan kaso da laifin neman matar aure

Kotu ta jefa wani mutum gidan kaso da laifin neman matar aure

Wata babbar kotun Masaka dake zaman ta a jihar Nasarawa, ta zartar da hukuncin dauri na watanni biyar a kan wani mai sana'ar fenti ɗan shekara 25, Aminu Usman, bisa aikata laifin neman matar aure.

Usman wanda mazaunin unguwar Mararraba ne a jihar, ya amsa laifin sa na neman matar aure, inda ya shaidawa kotun cewa ya aikata hakan ne a bisa rashin sani duk da gargaɗinsa da tayi na ya daina kiranta a wayar salula amma rashin yarda ta sanya ya ci gaba da aikata hakan.

Da sanadin kamfanin dillancin labarai na NAN, alkalin kotun Yakubu Ishaku, ya baiwa Usman zabin biyan tara ta Naira dubu bakwai a sakamakon neman afuwar kotu da yayi, ya kuma gargade shi akan bibiyar matan aure.

Kotu ta jefa wani mutum gidan kaso da laifin neman matar aure
Kotu ta jefa wani mutum gidan kaso da laifin neman matar aure

Frank Swem, jami'in ɗan sanda mai shigar da ƙara ya bayyana kotun cewa, mijin wannan mata Umar Ibrahim, shine ya shigar da ƙorafi a ofishin 'yan sanda bayan sahibarsa, Zainab, ta labarta masa abinda ke wakana.

KARANTA KUMA: 'Yan bautar ƙasa biyu sun haihu a sansaninsu na hidima

Jami'in ɗan sanda ya ci gaba da cewa, "a duk lokacin da Usman ya kirayi Zainab, sai ya rinƙa yi mata furuci na sha'awar muryarta tare da neman yadda za a yi su hadu", inda hakan ya sanya mijin ya shirya masa tarko kuma ya afka cikin gaggawa.

A yayin haka kuma, wata kotun Kubwa, ta zartar da hukuncun ɗauri na watanni huɗu akan wani ɗan shekara 25, Sabi'u Ado, bisa aikata laifin satar jakunkunan yara na makaranta da bokitai guda uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng