An kori wani babban likita domin sata gadajen asibiti a Akwa Ibom
- Gwamnatin Akwa Ibom ta kori wani babban likita domin sata gadajen asibiti shida a jihar
- Kwamishinan kiwon lafiya ya ce likitan ya sace gadajen ne a watan Oktoba na bara
- Kwamishinan ya bayyana cewa asibitin na daya daga cikin mafi yawan asibitocin da ba su samun kula a jihar
Gwamnatin Akwa Ibom ta ce ta kori Dokta Nwaopara A.U, mai ba da shawara da kuma ma'aikatar kula da lafiya a asibitin Psychiatric da ke Eket, saboda zargin sace wasu gadajen asibiti shida da kuma canza su don amfanin kansa.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar, Dokta Dominic Ukpong, ya ba da sanarwar yayin da yake jawabi da masu kula da ma'aikatan asibitin a Eket ranar Juma'a, 18 ga watan Janairu.
Ya yi zargin cewa likitan ya sace gadajen ne a watan Oktoba na bara kuma ya mayar da su don yin amfani da shi a asibitinsa da ke yankin Marina na Eket.
Amma Dakta Nwaopara ya bayyana cewa al'amarin yana gaban kotu.
KU KARANTA: Kimiyya da Kiwon Lafiya: An gano sabuwar hanyar ganin mafarin cutar daji, wato Kansa
"Mun sallami likita wanda ya sace gadaje a asibiti na psychiatric kuma ya canza su zuwa ga yin amfani da su”.
"Ba za mu yarda da irin wannan hali daga kowane likita ba. Ina son in gode wa masu kula da al’amuran asibitin don hadin gwiwa a lokacin bincike", in ji Ukpong.
Legit.ng ta tattaro cewa, kwamishinan ya lura cewa asibitin na daya daga cikin mafi yawan asibitocin da ba su samun kyakyawar kula a jihar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng