Kamfanin mai na NNPC yace baya bukatar sahalewar majalisa kafin ya yi tallafin mai

Kamfanin mai na NNPC yace baya bukatar sahalewar majalisa kafin ya yi tallafin mai

- Kamfanin mai na NNPC ya mayar wa da majalisa martani

- Har yanzu ba'a daina wahalar mai ba

- Kamfanin yace yana kashe biliyan daya na naira a kullum kan tallafi

Kamfanin mai na NNPC ya ce baya bukatar sahalewar majalisa kafin ya yi tallafin mai
Kamfanin mai na NNPC ya ce baya bukatar sahalewar majalisa kafin ya yi tallafin mai

Martanin kamfann NNPC ga majalisa dai mai kaushi ne, nayan wahalar mai da aka sha wata kusan na uku kenan.

Kamfanin na NNPC yace baya bukatar sahalewar majalisar wakilai ko dattijai kafin ya saka kudi domin tallafin man fetur, wanda a da gwamnatin ta ce ta cire.

A yanzu dai shugaban kamfanin mai na NNPC, MAi Kanti Baru, da ministan mai Kachiku, sun ce akalla biliyan daya ta naira a kullum suke kashewa domin tallain mai ga 'yan Najeriya, domin sayar da shi a farashin gwamnati na N143-N145.

DUBA WANNAN: MAsana sun gan yadda zasu shawo kan cutar kansa

Wannan na zuwa ke da wuta, sai majalisar tace ai babu wani kasafi da suka iyar na tallafi, don haka ba bisa k'ida ba kamfanin da ma'aikatar ke kashe biliyan daya a kullum.

Sai dai kamfanin ya ce shugaba Buhsri shine babban ministan man fetur, kuma sahalewarsa a kashe kudin ta bayan fage domin mai ya samu, ta wadatar, ba sai majalisa ta bi kadi ba.

Har yanzu dai ana wahalar mai, inda kuma aka same shi, yakan haura naira 200-300.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng