Nejeriya ta samu gagarumin ci gaba a fannin noma - Inji shugaba Buhari
- Shugaba Buhari ya bayyana nasarar da kasar ta samu a fannin noma
- Ya ce mutane da dama sun tsunduma a harkan noma musamman matasa
- Ya bayyana hakan ne a lokacin day a karbi bakuincin daya daga cikin sababbin jakadun kasar waje
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya jadadda cewa kasar Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a harkar noma a fadin kasar.
A cewar shugaban kasar a halin da ake ciki mutane da dama musamman matasa sun shiga cikin harkar ba kama hannun yaro.
Shugaban ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin Jakadan kasar Bangaladash, Manjo Janar Kazi Sharif Kaikoband a fadarsa da ke Abuja.
KU KARANTA KUMA: Zan ziyarci Kano duk da adawa - Kwankwaso
Shugaba Buhari ya nuna cewa a halin yanzu Najeriya ta rage shigowa da kayayyakin abinci daga waje a maimakon haka, tana kokarin ganin tana fitar da abinci da ta noma zuwa kasashen ketare.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng