Matan Musulmi da Kirista sun gudanar da addu’a na musamman ga Najeriya a Kafanchan
- Kungiyar matan Musulmi da Kirista sun gudanar da addu'o'i na musamman an garin Kafanchan
- An gudanar da addu'o'in ne domin wanzuwar zaman lafiya a fadin kasar
- An kuma karanta Al-Qur'ani mai girma da littafin Injila
Farfesa Kabiru Mato, kwamishinan karamar hukumar da al’amuran shugabanci a jihar Kaduna, ya bukaci mata da su fara gudanar hakkinsu a matsayinsu na iyaye sannan su zamo kan gaba wajen wanzar da zaman lafiya a kasar.
Ya yi wannan kira ne a wajen wani addu’a na musamman da kungiyar matan Musulmi da Kirista suka gudanar domin zaman lafiya a kasar, a Kaduna a ranar Juma’a.
A wani sako na fatan alkhairi ga shirin, Alhaji Yusuf Mu’azu, mai tafiyar da karamar hukumar Jema’a, ya yaba ma matan bisa goyon baya da suke ba gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya a garuruwansu.
Hajiya Amina Kazaure, kakakin kungiyar, ta ce kungiyar na shirin ilimantar da mata akan rawar ganinsu ga gwamnati wajen ganin an samuzaman lafiya.
KU KARANTA KUMA: Nade-naden Shugaban Kasa Buhari sun bar baya da kura
Sir Anne Falola, daraktan kungiyar tace kungiyar wacce ke dauke da sama da Musulmai da Kirista 30 na dauke da kudirin yin aiki tare domin magance matsalolin al’umma.
Anyi karatun Al-Qur’ani mai girma da littafin injila, sannan kuma an gudanar da addu’o’i na zaman lafiya a Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng