Dandalin Kannywood: Diyar marigayi Dan Ibro zata zama amarya gobe

Dandalin Kannywood: Diyar marigayi Dan Ibro zata zama amarya gobe

Diya ga fitaccen jarumin nan marigari Rabilu Musa Danlasan da aka fi sani da Ibro mai suna Jawahir Rabilu Musa za ta amarce a gobe goben nan ranar Asabar, 20 ga watan Janairun wannan shekarar.

Kamar dai yadda muka samu, Jawahir Rabilu Musa za'a daura mata aure ne da sahibinta mai suna Isah Saleh a gobe asabar din a garin Danlasan dake a karamar hukumar Warawa ta jihar Kano din.

Dandalin Kannywood: Diyar marigayi Dan Ibro zata zama amarya gobe
Dandalin Kannywood: Diyar marigayi Dan Ibro zata zama amarya gobe

Legit.ng ta samu cewa haka zalika ga masu sha'awar zuwa daurin auren za su hadu ne a unguwar Zoo Road a layin gidan Dan Asabe inda daga nan ne ake sa ran mutane za su dunguwa zuwa wurin daurin auren.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Allah yayi wa jarumin rasuwa ne a shekarun baya.

A wani labarin kuma, Fitaccen jarumin nan na wasan fina-finan Hausa mai suna Tijjani Asase ya wallafa budaddiyar wasika zuwa ga daukacin abokan sana'ar sa dake a masana'antar ta Kannywood inda ya bayyana ra'ayin sa game da al'amurra da dama.

Jarumin dai ya rubuta sannan kuma ya wallafa wasikar ne a kafafen sadarwar zamani da mutane ke tu'ammali da su na Facebook, Tuwita da kuma Intagram.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng