Dandalin Kannywood: Tijjani Asase ya wallafa budaddiyar wasika zuwa ga yan wasan Hausa

Dandalin Kannywood: Tijjani Asase ya wallafa budaddiyar wasika zuwa ga yan wasan Hausa

Fitaccen jarumin nan na wasan fina-finan Hausa mai suna Tijjani Asase ya wallafa budaddiyar wasika zuwa ga daukacin abokan sana'ar sa dake a masana'antar ta Kannywood inda ya bayyana ra'ayin sa game da al'amurra da dama.

Jarumin dai ya rubuta sannan kuma ya wallafa wasikar ne a kafafen sadarwar zamani da mutane ke tu'ammali da su na Facebook, Tuwita da kuma Intagram.

Ga dai wasikar nan kamar yadda ya rubuta ta:

Dandalin Kannywood: Tijjani Asase ya wallafa budaddiyar wasika zuwa ga yan wasan Hausa
Dandalin Kannywood: Tijjani Asase ya wallafa budaddiyar wasika zuwa ga yan wasan Hausa

'Wasika zuwaga yan wasan kwaikwayo ni Tijjani asase ba kazami bane kuma bantaba jawo ma masana'antar film wani Abu ba. Amman lokacin mulkin rabo sai da na bar mahaifata, duk san da nake wa kano sai da na barta. Kuma a wancan mulkin banga abun da aka samu na cigaba ba, sai dai ci baya.

Ci bayan da shine yaran da aka kora daga kano suka koma wasu gari suka zama karuwai .muka zo mulkin kwankwaso aka bawa belly mulkin censors board sannan muka dawo gida jen mu muka ciga ba da sana'armu a gaban iyalinmu .

Allah ya kawo mu mulkin ganduje aka dau Dan cikinmu akabashi kujerar board. Daga lokacin da yazama zuwa yanzu yasa akayi LGA 44 yasa Gwamnati tayi wakilci kuma taba su office. Zamu iya tallata hajarmu . yasa aka de bemu aka sama mutum 300 yasa Gwamnati zata bamu mota ,yasa Gwamnati tayi mana kasuwa tamu takanmu, yaja goranci film village Allah baiyiba haka kawai sai wasu tsurarun mutane suke son shirin su lalata duk wani shirin da yazo da shi na cigaba .

Dan bukatar Kansu kuma suna kiran Kansu shugabanni . nasan mutun uku dasu keyin rigima da Afakallahu kuma tare suka taso kungiya daya har Allah yaba shi wannan kujerar daya kai a yanzu, kuma sai da suka shirya saboda akan gaskiya yake suma akanta suke. Kuma yanzu kowa ya gane matsalar . kuma sun yadda azo a gyara toh Ku rigamar Ku dakuke da afakallahu.

Shine ba kwaso agyara masana antar film. Kuma Kuma kuna kiran kanku jagworori toh wallahi muna kallanku. Duk sohon da baji kunyar hawa jaki ba toh wlhi bazai ji kunyar kada shi ba. Allah duk mutumun da baya son cigaban wannan masa na antar Allah ya fitar da shi daga ckinmu. Idan da abuncinsa aciki Allah ka to she. Wannan ra ayin tijjani asase ne bara ayin wani bane"

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng