Zaben kananan hukumomi: Jam'iyyar APC ta fada cikin cakwakiya a wannan jihar

Zaben kananan hukumomi: Jam'iyyar APC ta fada cikin cakwakiya a wannan jihar

Yayin da ake ta shire-shiren gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar Edo dake a yankin Kudu maso Kudancin kasar nan a farkon watan Maris mai zuwa, alamun barkewar rikici na ta kara bayyana a cikin jam'iyyar APC mai mulki a jihar.

Wannan dai na faruwa ne a dalilin wata sabuwar dokar da aka kakaba ta haramcin tsayawa takara ga dukkan wanda ya taba rike mukamai a kananan hukumomin da suka hada da shugaban karamar hukuma, kansila da ma shugabannin jam'iyyar.

Zaben kananan hukumomi: Jam'iyyar APC ta fada cikin cakwakiya a wannan jihar
Zaben kananan hukumomi: Jam'iyyar APC ta fada cikin cakwakiya a wannan jihar

Legit.ng ta samu dai cewa wannan matakin ko kadan bai yi wa 'yayan jam'iyyar dadi ba sai dai kuma ita jam'iyyar ta dage akan tabbas ba zata janye wannan dokar ba.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu mai sosa zuciya yanzu haka daga majiyar mu shine wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun sake sacewa tare da yin garkuwa da wasu farar fata 'yan kasar waje.

Kamar dai yadda muka samu, majiyar ta mu ta tabbatar da cewa an sace mutanen ne a kan hanyar nan ta Abuja zuwa Kaduna bayan sun samu nasarar kashe dan sandan dake yi masu rakiya a daren jiya Alhamis.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng