Korar malamai: Kungiyar malaman makaranta ta bayar da dalilin janye yajin aikin da ta shiga

Korar malamai: Kungiyar malaman makaranta ta bayar da dalilin janye yajin aikin da ta shiga

A jiya ne dai kungiyar malaman makarantar firamare dake a jihar Kaduna watau Nigeria Union of Teachers a turance ta sanar da matsayar janye yajin aikin da ta shiga na har sai- baba-ta-gani sannan ta kuma umurci dukkan 'ya'yan ta da su koma bakin aikin su.

Shugaban kungiyar dai reshen jihar mai suna Mista Audi Amba ne ya sanar da hakan jim kadan bayan kammala wani zama na gaggawa da suka yi da majalisar zartarwar jihar kan lamarin a garin Kaduna, babban birnin jihar.

Korar malamai: Kungiyar malaman makaranta ta bayar da dalilin janye yajin aikin da ta shiga
Korar malamai: Kungiyar malaman makaranta ta bayar da dalilin janye yajin aikin da ta shiga

Legit.ng dai ta samu cewa kadan daga cikin dalilan da kungiyar ta bayar na janye yajin aikin shine a cewar su yanzu Gwamnan ya bayar da dama ga dukkan korarrun malaman na samun kyakkyawar rayuwa ta fannin tattalin arziki.

Kungiyar ta bayyana jin dadi game da sabon shirin da gwamnatin ta jihar ta bullo da shi domin taimakawa dukkan wadanda aka kora kuma masu sha'awa neman bashi mai saukin kudin ruwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng