Wani Dansanda ya kira ruwa bashi da lema a yayin taƙaddama tsakaninsa da Dan Achaba
- Wani Dansanda ya shiga mawuyacin hali yayin da Dan Achaba ya sume a hannunsa
- Dansanda ya doki dan Achabar ne da kulki saboda ya hana shi N50 na goro
Sau dayawa, kasassabar mu ta mutane ce ke janyo mana rigima, wanda ya kan jefa mu cikin mawuyacin hali, kamar yadda ya faru a Onitsha na jihar Anambra, tsakanin wani Dansanda da Dan Achaba.
Shi dai wannan Dansanda mai suna Kofur Emmanuel ya nemi wani dan achaba da ba’a bayyana sunan shi ba ya bashi na goro, N50, amma shi kuwa dan achaban ya kekashe kasa, yace akan me? Ban ci ba, ban sha ba, haka nan in dauki naira hamsin in baka.
KU KARANTA: Buhari ya lashi takobin ladabtar da duk masu shirin tayar da zauni tsaye a 2019
Abinka da mai jiran kadan, nan da nan Dansanda ya harzuka, inda yayi ma dan achaba kwaf daya da kulkinsa, aikuwa nan take Dan Achaba ya fadi sumamme, ji kake tim! Kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.
Ba sa gogan naka ya rikice ba, ya daburce gaba daya, yana ta kokarin farfado da Dan Achaban, yayi yayi, har ya gaji, da yaga babu Sarki sai Allah, sai ya sa kuwwa, yana kiran jama’a su kawo masa agaji, duk jikinsa yayi sanyi, tsoronsa kada dan achaban ya mutu, don kuwa ya san jama’an wajen kashe shi zasu yi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng