Babbar Magana: An maka Laftanal Janar Yusuf Buratai kotu

Babbar Magana: An maka Laftanal Janar Yusuf Buratai kotu

Kotun daukaka kara dake zaman ta a garin Abuja, babban birnin tarayya a jiya ta tsayar da ranar 15 ga watan Maris mai kamawa a matsayin ranar da zata fara sauraren karar da wani soja da aka kora mai suna Manjo Janar Ibrahim Sani ya shigar a gabanta yana kalubalantar hukuncin.

A baya dai cikin wata Yulin da ya gabata ne dai wasu manyan sojoji da suka hada da Laftanal Janar Tukur Buratai suka tabbatar da samun Manjo Janar ibrahim din da laifi dumu-dumu tare da karya wata dokar rundunar game da wani filin da ake zargin sa da tafkawa.

Babbar Magana: An maka Laftanal Janar Yusuf Buratai kotu

Babbar Magana: An maka Laftanal Janar Yusuf Buratai kotu

Legit.ng ta samu dai cewa sakamakon haka ne yasa rundunar ta rage masa matsayi daga Manjo Janar ya zuwa Birgediya janar sannan ta kuma umurci ya biya wasu sojojin makudan kudaden fansa.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu mai sosa zuciya yanzu haka daga majiyar mu shine wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun sake sacewa tare da yin garkuwa da wasu farar fata 'yan kasar waje.

Kamar dai yadda muka samu, majiyar ta mu ta tabbatar da cewa an sace mutanen ne a kan hanyar nan ta Abuja zuwa Kaduna bayan sun samu nasarar kashe dan sandan dake yi masu rakiya a daren jiya Alhamis.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel