Bugun dalibai: An kori shugaban makaranta da wasu malamai 3 a jihar Nasarawa

Bugun dalibai: An kori shugaban makaranta da wasu malamai 3 a jihar Nasarawa

Labarin da muke samu yanzu na nuni ne da cewa ma'aikatar ilimi ta jihar Nasarawa ta sanar da korar shugaban makarantar Sakandiren nan ta garin Eggon tare da wasu malamai su uku bisa dukan daliban su da suka yi da ya wuce misali.

Kwamishinan ilimi na jihar Malam Tijjani Ahmed shine ya sanar da hakan ga manema labarai a jiya garin Lafiya babban birnin jihar inda ya bayyana cewa tuni su sun haramta irin dukan nan ga daliban jihar.

Bugun dalibai: An kori shugaban makaranta da wasu malamai 3 a jihar Nasarawa
Bugun dalibai: An kori shugaban makaranta da wasu malamai 3 a jihar Nasarawa

Legit.ng dai ta samu cewa a satin da ya gabata ne dai wani faifan bidiyo na dukan daliban yayi ta yawo a kafafen sadarwar zamani wanda kuma ya jazawa jihar tofin Allah-tsine daga jama'a da dama.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu mai sosa zuciya yanzu haka daga majiyar mu shine wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun sake sacewa tare da yin garkuwa da wasu farar fata 'yan kasar waje.

Kamar dai yadda muka samu, majiyar ta mu ta tabbatar da cewa an sace mutanen ne a kan hanyar nan ta Abuja zuwa Kaduna bayan sun samu nasarar kashe dan sandan dake yi masu rakiya a daren jiya Alhamis.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng