Kungiyar Dattawan Arewa ta naɗa Alhaji Sani Zangon Daura a matsayin sabon shugabanta

Kungiyar Dattawan Arewa ta naɗa Alhaji Sani Zangon Daura a matsayin sabon shugabanta

Kungiyar Dattawa yankin Arewa ta sanar tsohon minista Alhaji Sani Zangon Daura a matsayin sabon shugabanta biyo bayan murabus da tsohon shugabanta, Paul Unongo yayi.

Kungiyar ta sanar da sauyin ne a ranar Alhamis 18 ga watan Janairu, inda ta bayyana cewa hakan ya zama wajibi duba da abubuwan dake faruwa a Najeriya, musamman kashe kashen da ake yi a jihohin Benuwe, Taraba, Adamawa, Kaduna, Zamfara, da ma sauran yankin kasar.

KU KARANTA: Buhari ya lashi takobin ladabtar da duk masu shirin tayar da zauni tsaye a 2019

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tsohon shugaban yayi murabus ne biyo bayan zargin tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakara da daukan nauyin hare haren makiyaya, wanda yayi sanadiyyar mutane da dama, inda yace zai dauki nauyin wasu Sojoji na daban da zasu yake makiyayan.Sai dai Atiku ya musanta wannan zargi, sa’annan yayi barazanar shigar da Unongo Kotu’

Kungiyar Dattawan Arewa ta naɗa Alhaji Sani Zangon Daura a matsayin sabon shugabanta

Alhaji Sani Zangon Daura

Mista Unongo ya dare mukamin shugaban kungiyar ne bayan rasuwar tsohon shugabanta, Alhaji Maitama Sule. Kaakakn kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana godiyar kungiyar ga Unongo bisa gudunmuwar daya baiwa kungiyar, kumaya nuna alhinisu da murabus din da yayi.

“Kungiyar nan ta nada mataimakin shugabanta, Sani Zangon Daura a matsayin shugabanta, yayin da sauran sauye sauyen shuwagabanni zai wakana cikin yan kwanaki kadan.” Inji Ango.

Paul Unongo

Paul Unongo

Daga karshe, Kaakakin ya jajanta ma mutanen da suka rasa yan’uwansu sakamakon rikicin makiyaya da manoma, inda ya bukaci hukumomi dasu dage wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, sa’annan yayi kira ga jama’a da su kasance masu kula da sa ido kan duk wasu mutanen da basu san su ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel