Gobara ta lashe gidan mataimakin gwamnan jihar Imo

Gobara ta lashe gidan mataimakin gwamnan jihar Imo

Kimanin gidaje biyar ne gobara ta lashe a ranakun laraba da alhamis din da suka gabata a wurare daban-daban a birnin Owerri na jihar Imo, wanda sun hadar har da gidan mataimakin gwamnan jihar, Eze Madumere.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Andrew Enwerem, ya tabbatarwa manema labarai afkuwar wannan annoba, inda yace an yi sa'a babu ko rai daya da ya salwanta a gidaje biyar din da wuta ta lashe.

Gobara ta lashe gidan mataimakin gwamnan jihar Imo
Gobara ta lashe gidan mataimakin gwamnan jihar Imo

Rahotanni da sanadin jaridar The Punch sun bayyana cewa, wannan gobarar ta afku ne da sanadin kone-kone yayi da kuma shara da mazauna ke yi, inda ta laso gidan mataimakin gwamnan dake Ibari Ogwa.

KARANTA KUMA: Kotu ta yanke wa shugaban ƙungiyar haɗin kan malaman musulunci hukuncin ɗaurin rai da rai

Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Uche Onwuchekwa ya bayyanawa manema labari cewa, dukiya ta kimanin N10m da ta hadar da mota mallakin maigidansa ta salwanta a gobarar.

Onwuchekwa ya ci gaba da cewa, kone-kone yayi da shara a gewayen gidan ita ta sanadiyar gobarar domin kuwa babu kayayyakin wutar lantarki ko guda da ke kunne a gidan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng