Labari da dumi-dumi: Wani gwamna ya yi zazzaga, ya sauke dukkanin masu rike da mukaman siyasa a jihar sa
- Gwamnan jihar Kwara ya sauke dukkanin masu rike da mukaman siyasa a jihar
- Hukuncin ya shafi harda masu bawa gwamna shawara na musamman
- Gwamnan ya yi masu fatan alheri a aiyukan su na gaba
Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya dauke dukkanin masu rike da mukaman siyasa a jihar. Sanarwar da sakataren gwamnatin jihar ya fitar ta ce hukuncin ya shafi har da masu taimakawa gwamna na musamman.
DUBA WANNAN: Ba mu da hannu cikin harin Benuwe, Inji kungiyar Miyetti Allah
Gwamnan ya umarci kwamishinonin jihar da su mika ragamar tafikar da ma'aikatun da suke jagoranta ga manyan sakatarori dake wurin. Kazalika sanarwar ta ce gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da harkokin gwamnati sun cigaba da tafiya yadda ya kamata kafin a nada sabbin kwamishinoni.
Ahmed ya yi fatan alheri ga tsofin hadiman gwamnatin tare da yi masu addu'ar yin gamo da babban rabo.
Gwamnatin jihar ba ta bayar da dalilin yin zazzagar ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng