Kotu ta yanke wa shugaban ƙungiyar haɗin kan malaman musulunci hukuncin ɗaurin rai da rai
Shehun malami kuma shugaban ƙungiyar haɗin kan malaman musulunci na duniya, Yusuf Alƙaradawi, zai fuskanci hukuncin ɗaurin rai da rai kamar yadda wata kotun soji a ƙasar Masar ta zartar.
Rahotanni da sanadin shafin Temmuz sun bayyana cewa, babban malamin zai fusakanci wannan hukunci ne tare da wasu mutane 17 da ake tuhumarsu da yunƙurin kashe wani babban jami'in soja Kanal Wa'il Tahun, tun a shekarar 2015 a birnin Alƙahira.
Shafin na Temmuz ya ruwaito cewa, ana tuhumar shehin malamin da laifi na yunƙuri kisan kai, tunzarar da al'umma tare da yaɗa labarai na shaci faɗi.
KARANTA KUMA: Hukumar DPR ta rabar da lita 14, 400 ta man fetur kyauta a Abuja
Legit.ng ta fahimci cewa, kotun ta soji ta kuma zartar da hukunci zama a gidan kaso har na tsawon shekaru 26 a kan wasu mambobin ƙungiyar da suka haɗar da; Abdurrahman el-Berr, Mahmud Gazlan, Taha Vahdan da kuma Said Uleyva.
Kotun ta kuma yaye ƙarar da ke kan wani mamba na ƙungiyar, Muhammad Kamal, a sakamakon ajali da yayi masa halinsa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng