Zaben 2019: Shugaba Buhari ya yabi tsohon shugaban kasa Jonathan
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi jan hankali ga al'ummar kasar nan ta Najeriya da su guji dukkan abun da zai jawo tashin hankali a zabukan shekarar 2019 mai zuwa.
Haka zalika shugaban kasar ta Najeriya ya bayyana cewa hakika tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya taka rawar gani musamman ma wajen ganin ya gabatar da sahihin zaben sannan kuma ya mika mulki yayin da sakamakon ya fita.
Legit.ng ta samu dai cewa shugaban dai yayi wannan maganar ne kwanaki kadan bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission INEC aturance ta fitar da jadawalin yadda zaben zai kasance.
A wani labarin kuma, mun samu cewa Daga karshe dai majalisar wakillan Najeriya a jiya ta zartar da kudurin dokar nan da aka dade ana tsammani na bangaren harkokin man fetur watau Petroleum Industry Governance Bill, PIGB a turance.
Wannan dai ya na nuni kenan da cewa yanzu za'a yi wa bangaren na harkallar mai a matakin gwamnatin tarayya garambawul da kuma ake sa ran zai kawo sauye-sauye masu ma'ana da dama.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng