'In Buhari yaso zai iya dakatar da hare-haren makiyaya' - SERAP
- Kungiyar SERAP ta soki shugaba buhari na nuna halin ko in kula da yake game da kasheshen da yake faruwa tsakanin Fulani makiyaya da manoma a jihar Binuwe
- Kungiyar ta ce shirun da shugaba buharin yayi yana ta Kano cece kuce tsakanin al’umma, inda suke ganin kaman yana basu kariya ne
A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan SERAP yayi ranar laraban nan data gabata ya bukaci shugaba buhari daya hukunta wanda aka samu da hannu a cikin wannan ta’asar sannan kuma abiwa wanda abin ya shafa haqqin su.
A talatar data gabata ne ‘yan majalisar dattijai da majalisar wakilai, suka yanke hukuncin kisa ga dukkan wanda aka kama da hannu a cikin wannan lamari. Har ila yau majalisar dattijai ta bawa shugaban ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris kwanaki 14 akan ya gurfanar da dukkan wanda suke da hannu a ciki.
Nuna halin ko in kula da shugaba buhari yayi shine yake ta Kara kawo cece kuce tsakanin al’umma, inda da yawa suke ganin kaman shugaba buhari shine yake bawa wadannan masu ta’asar kariya.
Kungiyar SERAP ta tabbatar da cewa, shugaba buhari a matsayin shi na shugaban kasa mai cikakken iko, shine yake da damar da zai tsayar da dukkanin kasheshen da kuma bata dukiyoyin jama’a da Fulani makiyaya suke a fadin kasar nan. Inda tace shugaba buhari yana bukatar yayi magana da yan Najeriya musamman ma ga iyalan wanda abin ya shafa.
Har yanxu gwamnati bata yi wani kokari na magance hare-haren da ake kaiwa yankunan Benuwe, Taraba, Adamawa da sauran sassa na kasar nan, sannan sun manta da halin da al’ummar yankunan suke ciki. Kungiyar ta bukaci shugaba buhari daya tabbatar da adalci a kasar nan, da kuma daukan mataki wanda suka dace.
DUBA WANNAN: An yaye dalibai 72 da zasu tuka jiragen saman sojin Najeriya
Yana da mutukar muhimmanci al’umma su dinga zama shaida akan hukuncin da ake yanke wa dukkanin masu tada kayar baya, musamman masu kashe kashe da kone dukiyar jama’a.
A kwanakin baya majiyar mu ta rawaito cewar Farfesa Wole Soyinka, a cikin wani littafi da ya rubuta da ya kirashi da suna “Impunity Rides Again” inda ya soki shugaba buhari akan gazawar gwamnatin sa tayi akan Fulani makiyaya.
Shugaban hukumar ‘yan sanda na Najeriya ya sanya Kwamishinan yan sanda na jihar benuwe din Bashir Makama, domin magance matsalar tsaro a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng