Mata da maigidanta ya ki saduwa da ita shekaru uku ta sami sauki daga alkali

Mata da maigidanta ya ki saduwa da ita shekaru uku ta sami sauki daga alkali

- Ya gudu yadaina saduwa dani bayan na haifa mana yara biyu

- Nasha kama shi da farkarsa

- Alkali ya raba auren

Mata da maigidanta ya ki saduwa da ita shekaru uku ta sami sauki daga alkali

Mata da maigidanta ya ki saduwa da ita shekaru uku ta sami sauki daga alkali

Wata kotu ta Idi-Ogungun Customary Court a Agodi a Ibadan jihar Oyo ta warware auren shekaru 12 wanda wata baiwar Allah mai suna Raliyat Ajila mai shekaru 36 da haihuwa ta shigar.

Shekaru ta kwashe zaman hoho, bayan da mijinta ya ki zuwa shimfidarta tsawon shekaru uku sai neman mata a waje.

Alkali ya warware auren bayan mai kai kara ta bada hujjojin kama shi mijin da take da matan gari, da ma kuma kara aure da tarewa a wani gida da yagina, bayann ya barta da yaransu a gidan haya ba abinci.

DUBA WANNAN: An harbi mai cikki bisa kuskure a yayin fasa taro

Raliya ta kuma bada hujjar cewa har fitsarin jini yake a lokacin iskancin nasa saboda cuta da ya debo, amma ta jure ta zauna dashi domin samun maslaha, ta kuma kula da shi, amma yana warkewa ya koma ruwa.

Shi dai mijin a kokarin kare kansa ya ce tsinuwa da zagi da take ta yi masa yasa ya rasa aikinsa, aka kore shi, shi kuma don haka ya daina biya mata bukatunta na aure, yake fafutukarsa a waje.

An dai raba wannan auren a dazu, kuma Chief Mukaila Balogun ya ce dole Ajila ya dinga biya 7,000 duk wata domin ciyar da yaransa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel