Sanata Abubakar Bukola Saraki ya rantsar da sabon Sanatan Najeriya (Hotuna)
Shugaban majalisar dattajai, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya rantsar da sabon sanata daga jami’iyyar APGA a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, inji rahoton gidan talabijin na Channels.
Wannan Sanata ya fito ne daga mazabar Anambra ta tsakiya, Sanata Victor Umeh ya samu nasara zaben daya gudana ne a satin daya gabata, inda ya samu kuri’a 64,879, yayin da abokan karawarsa basu samu kuri’a ko dubu day aba.
KU KARANTA: Yansanda sun damƙe matar da ta yanka boyi boyin gidanta a Ogun
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Saraki ya rantsar da Sanata Umeh ne a farfajiyar majalisar, biyo bayan samun takardar shaidar lashe zaben daya fafata a ciki daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC.
Sabon Sanatan, wanda shine shugaban jam’iyyar APGA ya samu rakiyar Matarsa da sauran manyan jam’iyyar tasu, tare da magoya bayansa, hakan ya sanya shi zama Sanata daya tilo daga jam’iyyar adawa ta APGA.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng