Wutar lantarki ta aika da wani mutumi lahira yayin da yake kokarin satar wayoyin lantarki
- Ya mutu a wulakance a kan falwayar wuta a garin Jos
- Ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da yayi yunkurin satar wayar wuta
Wani barawon wayoyin wutan lantarki ya gamu da ajalinsa a daren Alhamis, 18 ga watan Janairu sanadiyyar wutan lantarki daya shafe shi a kan falwa, a unguwar Bukuru, garin Jos inji rahoton TVC.
Barawon da ba’a bayyana sunansa ba ya mutu ne sa’adda ya hau kan falwaya, don ya cire wasu wayoyi da na’urorin daga cikin tiransifoma dake sama, amma abinka da ajali, idan yayi kira, ko ba dalili sai anje, kwatsam sai aka samu akasi, wutar ta shafe shi, nan da nan ya mutu.
KU KARANTA: Yansanda sun damƙe matar da ta yanka boyi boyin gidanta a Ogun
Majiyar Legit.ng ta ruwaito da kyar jama’a suka kwanto gawarsa daga saman, saboda wutar ta makalar da shi tun a cikin dare, har sai da safiyar Alhamis din aka sako shi, wanda hakan yayi sanadiyyar dauke wuta a unguwar.
Majiyar ta ruwaito jama’an unguwar suna kokawa kan yawan sace sacen na’urorin lantarki daya yawaita a unguwar, don haka ne ma suka mayar da Tiransifomar tasu sama, amma duk da haka basu sha ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng