Abuja: Za mu rage kashi 50 cikin dari na haɗari a kan hanyoyi a 2018 – In ji FRSC

Abuja: Za mu rage kashi 50 cikin dari na haɗari a kan hanyoyi a 2018 – In ji FRSC

- Hukumar FRSC ta yi alwashin rage kashi 50 cikin dari na haɗari a kan hanyoyi a shekarar 2018

- Hukumar ta sanar hakan ne yayin da ta ke kare tallafin kudi a gaban kwamitin majalisar dattijai a Abuja

- Shugaban hukumar ya za su horar da hukumomi masu kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihohi don inganta kwarewarsu

Shugaban hukumar tabbatar da tsaron hanyar mota (FRSC), Mista Boboye Oyeyemi ya bayyana cewa hukumar za ta rage kashi 50 cikin dari na haɗari a kan hanyoyi idan an ba da kuɗin da aka rubuta wa hukumar.

Ya sanar da wannan a yayin da hukumar ke kare tallafin kudi a gaban wani kwamitin majalisar dattijai wanda sanata Tijjani Kaura ya jagoranta a ranar Laraba, 17 ga watan Janairu a Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa, Oyeyemi wanda ya bayyana cewa hukumar za ta cimma wannan burin ta hanyar manufofinta kuma ya lura cewa hukumar za ta horar da hukumomi masu kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihohi don inganta kwarewarsu.

Abuja: Za mu rage kashi 50 cikin dari na haɗari a kan hanyoyi a 2018 – In ji FRSC
Mista Boboye Oyeyemi

‘Yan majalisar sun yaba wa FRSC saboda ci gaban da hukumar ta samu a raguwar hadarin hanyoyi a shekarar 2017.

KU KARANTA: Rundunar yan sandan jihar Kebbi sun kama gagaruman barayin mota 8

Amma har yanzu FRSC ba ta riga ta buga cikakken bayani game da hadarin hanyoyi na 2017 ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng