Yan majalisa na bincike akan kamun daliban Najeriya a kasar Indiya
Majalisan wakilai, a jiya, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta magance kame kame da rashin imani da ake aiwatarwa akan yan Najeriya masu karatu a kasar India.
Har ila yau majalisar ta bukaci ofishin jakadancin Najeriya a India da ta binciki hanyoyin diflomasiyya wajen tabbatar da cewa an saki wadanda aka kama kamar yanda ya dace ko kuma akan beli, yayinda ake cigaba da gudanar da bincike.
Majalisar ta yanke shawarar aikawa da tawaga zuwa kasar don bincike akan halin kiwon lafiya da kuma lafiyar kwakwalwan daliban da aka kama.
Yan majalisan sun yanke shawarar ne bayan amincewa da takarda mai taken “Bukatar bincike akan kame-kame, rashin imani da yin keta wajen hukunta daliban Najeriya da hukumomin yan sandan India ke yi,” wanda Fredrick Agbedi ya gabatar.
KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP na shirin yakar APC ta yanar gizo
Yayinda ake cigaba da batun, Agbedi ya tuno a baya cewa yan sanda sun kama wasu daliban Najeriya, wadanda suka hada da Chidiebube Chukwuma, Priscilla Sunday da Shola a ranar 30 ga watan Disamba 2017 a yankin Yapralin Telangana, ba tare da makoma zuwa ga dangantakar diflomasiyya.
Yayin amincewa da batun, majalisan ta umurci kwamitinta kan harkokin kasashen waje da ta yi bincike akan dalilai da ya janyo rashin imanin yan sanda, kame-kame da hukunta daliban Najeriya .
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng