Rundunar yan sandan jihar Kebbi sun kama gagaruman barayin mota 8

Rundunar yan sandan jihar Kebbi sun kama gagaruman barayin mota 8

Jami'an yan sanda sun kama ya kungiyar fashi da makami takwas wadanda suka shahara wajen kwace mota da mashin a jihar Kebbi.

Rundunan yan sanda na musamman a yankunan Gwandu, Jega da Maiyama a jihar ne suka kama su, an kuma bayyana sunayen wasu daga cikinsu a matsayin Buhari Aminu, Muhammed Jafar da Ahmad Abubakar.

Yayinda aka bayyanasu a reshen yan sanda dake Birnin Kebbi, kwamishinan yan sanda, Ibrahim M. Kabiru, ya ce Aminu da sauran mambobin kungiyarsa sun kai hari gidan wani mai suna Alhaji Modi Gwandu a Gwandu inda suka amshe kudade, wayoyin salula, motarshi da sauran kaddarori.

Ya kara da cewa yan sandan sun samu labari ne, sannan suka shiga aiki inda suka yi nasarar kame daya daga cikin yan fashin tare da motar da aka sace a Kaduna.

Rundunar yan sandan jihar Kebbi sun kama gagaruman barayin mota 8
Rundunar yan sandan jihar Kebbi sun kama gagaruman barayin mota 8

KU KARANTA KUMA: Zai yi matukar wahala Buhari ya sake nasarar zabe a 2019 - Sheikh Gumi

Har ila yau, ya ce bisa ga bayanai, an kama Abubakar a yankin Maiyama a jihar tare da motar sata mai shigen Honda Civic.

“A yayin bincikenmu, mun kwato Karin motoci uku tare da mutane biyar wadanda ake zarginsu da hannu cikin harkar,” ya cigaba da cewa, yan sanda sun kama wani mai satar mashin mai suna Jafar, bayan ya dabawa wani mai suna Arzika Muhammed wuka sannan ya sace mishi mashin.

Ya ce mai laifin, wanda ya kasance cikin sunayen wadanda yan sandan ke farauta, ya yaudari mai mashin din da ya kaishi Birnin Kebbi daga Jega amman cikin tafiya ya daba mishi wuka sannan ya tafi da mashin din.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng