'Yan sanda sun damke wani shahararre mai garkuwa da mutane a Jigawa
- Hukumar ‘yan sanda a Jigawa ta cafke wani shahararre mai garkuwa da mutane a Jigawa
- Hukumar ta sanar cewa wanda ake zargin yana daya daga cikin sunayen wadanda rundunar ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo
- Mai magana da yawun hukumar ya ce an kama shi ne a lokacin da yake yunkurin cire kudi a wani banki da ke yankin hadeja
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Jigawa ta ce ta yi nasarar damke wani gawurtaccen mai sace mutane wadda ya addabi al’ummar jihar Akwa-Ibom, yankin kudu maso gabashin kasar.
Hukumar ta ci gaba da cewa , wanda ake tuhuma na daya daga cikin sunayen wadanda rundunar ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo tun watanni goma da suka wuce.
Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar, SP Abdul Jinjiri yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, 17 ga watan Janairu a birnin Dutse, ya bayyana sunan wanda ake zargi a matsayin Emmanuel Effiong Abang.
SP Jinjiri ya ce, an cafke shi ne a lokacin da yake yunkurin cire kudi a wani banki da ke yankin hadeja a jihar Jigawa.
KU KARANTA: Yansanda sun damƙe matar da ta yanka boyi boyin gidanta a Ogun
Haka kuma ya bayyana cewa, bincike ya tabbatar da cewa tun lokacin da rundunar ‘yan sanda ta fitar da sunayensu a matsayin masu laifi, ya gudu tare da fakewa a tsakanin yankin Nguru jihar Yobe da garin na Hadeja a jihar Jigawa.
Kakakin ya ci gaba da cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen wajen ganin an mayar da shi hannun hukumar ‘yan sanda a jihar ta Akwa-Ibom domin gurfanar da shi gaban kotu.
Jinjiri a karshekuma ya bayyana aniyar rundunar tasu wajen ci gaba da yin iya bakin kokarinsu domin tabbatar da tsaron dukiya da lafiyar al’umma baki daya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng