Gobarar tsakar dare ta janyo asarar jami’an Yansanda guda 3 da ýar Yarinya a Yola
- Yansandan Najeriya guda uku sun mutu a daki guda a barikin Yola
-Mutuwar ta auku ne sakamakon tashin gobara da tsakar dare
Rundunar Yansandan Najeriya, reshen jihar Adamawa ta tafka mummunan asara, inda jami’an ta guda uku suka rigamu gidan gaskiya biyo bayan wani hatsrain gobara daya rutsa dasu suna cikin barci da tsakar dare.
Wannan lamari mai muni ya faru ne a ranar Laraba 17 ga watan Janairu, sakamakon matsalar wutan lantarki da aka samu a barikin Yansanda dake Karewa a garin Yola, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwa wani sufetan Dansanda Bobboi, matarsa Grace, karamar yarinyarsu da kuma wani sabon kurta mai mukamin konstabul da aka dauka aiki.
KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin makiyaya da manoma
Daily Trust ta ruwaito duk kokarin da aka yin a ceto mamatan ya ci tura, a sanadiyyar karafan tsaro dake zagaye da tagogin gidan nasu, kamar yadda Kaakakin rundunar, SP Othman Abubakar.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin wadanda suka isa gidan akwai don nuna alhininsu akwai mataimakin gwamnan jihar Adamawa, Martins Babale, wanda ya jajanta ma rundunar Yansandan Najeriya sakamakon rashin da suka yi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng