Yansanda sun damƙe matar da ta yanka boyi boyin gidanta a Ogun

Yansanda sun damƙe matar da ta yanka boyi boyin gidanta a Ogun

Rundunar Yansandan jihar Ogun ta cafke wata mata mai suna Yewande Gbadebo kan zargin aikata mummunan laifi, inda ta yi amfani da wuka ta yanyanka jikin yar aikinta, mai shekaru 17.

Daily Truts ta ruwaitoUwargida Yewande, wanda daga cikin masu cin gajiyar taimakon matasa da aikin yin a N-Power ta tafka ma yarinyar wannan ta’asa ne biyo bayan bacewar wani burodi da ta siya, inda take ganin babu wanda zai sace shi, idan ba boyi boyin ba.

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin makiyaya da manoma

Bayan da uwargida Gbadebo ta gamsu a ranta boyi boyin ce ta cinya mata burod, sai ta saka wuka a cikin wuta, bayan da yayi zafi kuma sai ta yi amfani da shi wajen yanyanka jikin yarinyar mai suna Janet,kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Hukumar kare hakkin yara na jihar Ogun, CDHR, ne suka samu labarin wannan yarinya,inda suka kai karar matar ga Yansanda, su kuma Yansanda suka cika aikinsu, su ka bita har shagonta, suka yi ram da ita, a inda ta amsa laifinta ga hukumar.

Yarinyar ta shaida ma Yansanda cewa akalla ta kwashe shekaru 3 da uwardakin nata, amma bata taba barinta taje makaranta ba, ko kuma ta koyi sana’a ba.

KaakakinYansandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace zasu gurfanar da Matar da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel