Tashin hankali: An kashe Fulani Makiyayi a jihar Ekiti

Tashin hankali: An kashe Fulani Makiyayi a jihar Ekiti

- Allah ya kiyaye rikici a jihar Ekiti

- Yan garin sun kashe wani makiyayi a cikin daji

- Gwamnan ya yi ca a kan wannan abin da ya faru

An samu tashin hankali a unguwan Oke Ako da Irele a karamar hukumar Ikole na jihar Ekiti bisa ga kisan wani Makiyayi ranan Litinin.

An kashe makiyayin mai suna, Babuba Dengi, a cikin wani daji da ke tsakanin garuruwan guda biyu kuma ana zargin yan jihar Benue mazauna Ekiti ne suka aikata wannan aika-aika.

Tashin hankali: An kashe Fulani Makiyayi a jihar Ekiti
Tashin hankali: An kashe Fulani Makiyayi a jihar Ekiti

Wannan abu ya tilasta gwamnan jihar, Ayodele Fayose, ya kira ganawa na gaggawa a daren Talata a gidan gwamnatin jihar inda ya gargadi manoma da makiyaya a kan rikicin.

Gwamnan ya bada umurni ga jami’an tsaro a jihar su fito da makasan makiyayin kuma a gurfanar da su.

Fayose ya yi gargadi cewa ba za’a amince a kashe wani manomi ko makiyayi a jihar ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel