Jalingo: Gwamna Ishaku ya gargadi al'ummar Takum a kan ramuwar gayya

Jalingo: Gwamna Ishaku ya gargadi al'ummar Takum a kan ramuwar gayya

- Gwamnan Taraba ya gargadi al'ummar Takum a kan ramuwar gayya saboda mutuwar Hon. Hosea Ibi

Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a lokacin da shugabannin majalisar dokokin jihar suka masa ziyarar ta'aziyya

- Gwamnan ya bukaci jami'an tsaro su tabbatar da cewa an kama wadanda suka aikata wannan laifi da kuma gurfanar da su

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku a ranar Talata, 16 ga watan Janairu ya gargadi mazaunan garin Takum a kan zarge-zargen wani kabila saboda mutuwar Hosea Ibi, dan majalisar dokokin jihar.

Mista Ibi, wanda masu garkuwa da mutane suka sace a ranar 30 ga Disamba, 2017, daga baya kuma aka sami gawarsa a garinsu, Takum a ranar Litinin.

Mista Ishaku, wanda shi ma dan kabilar Jakun ne, ya yi wannan gargadin ne a lokacin da shugabannin majalisar dokokin jihar suka masa ziyarar ta'aziyya.

Jalingo: Gwamna Ishaku ya gargadi ‘yan kabilar Takum a kan ramuwar gayya

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku

A cewarsa, kisan gillar da aka yi wa dan majalisar wani babban laifi ne da kowane kabila ba ta yarda da ita ba.

KU KARANTA: Jalingo: Gwamna Ishaku ya saka dokar ta baci a Taraba

"Na riga na gargadi mutane game da ramuwar gayya ga ko wata kabila saboda wannan kisan ba maganar kabilanci bane”.

"Kada ku ce don an kashe wani Jukun, ku ma zaku dauka fansa”, in ji gwamnan.

Gwamna ya bukaci jami'an tsaro su tabbatar da cewa an kama wadanda suka aikata wannan mumunar laifi da kuma gurfanar da su.

Idan baku manta ba Legit.ng ta ruwaito cewa an tarar da gawar dan majalisar dokokin jihar ne a cikin gandun daji tsakanin iyakokin Taraba da Binuwai a ranar Litinnin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel