Badaƙalar N92m: Hukumar EFCC ta cafke ɗan tsohon gwamnan jihar Nasarawa

Badaƙalar N92m: Hukumar EFCC ta cafke ɗan tsohon gwamnan jihar Nasarawa

Hukumar yaki da rashawa ta kasa wato EFCC, ta gurfanar da Muhammad Adamu, ɗan tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu.

'Dan tsohon gwamnan ya gurfana a gaban mai shari'a J.K Dagat, na babbar kotun tarayya dake zamanta a jihar Kano tare da wani Felix Ojiako a ranar Laraba ta yau bisa zarginsu da aikata laifukan zambar makudan kuɗaɗe.

Hukumar ta bayar da wannan sanarwar ne da sanadin kakakin ta, Mista Samin Amaddin kamar yadda channels TV ta ruwaito.

Muhammad Adamu

Muhammad Adamu

Laifin Adamu ya bayyana ne a yayin da Atta Esin, shugaban kamfanin Biolocks Technology Limited yayi karar sa da cewa, Adamu yayi amfani da sunan kamfaninsa wajen aikata harkokin kasuwanci ba tare da masaniyarsa ba wanda da hakan ya janyowa kamfaninsa taruwar haraji har sama da naira miliyan daya.

KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sanda ta cafke barayin shanu da masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara

Hukumar EFCC ta bayyana cewa, a yayin da mai ƙorafi yayi iƙirarin harkar ta kimanin Naira miliyan 26 ce, bincike ya bayyana cewa ainihin harkar ta naira miliyan 92 ce.

Sai dai waɗanda ake tuhuma ba su amince da zargin da kotu take yi a kansu ba, inda mai shari'a Daggard ya ɗaga sauraron ƙarar zuwa ranar 7 ga watan Fabrairu, tare da bayar da umarnin ci gaba da tsare waɗanda ake tuhuma a karkashin kulawar hukumar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel