Sheikh Dahiru Bauchi ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin makiyaya da manoma
Babban Malamin addinin Musulunci a Najeriya , Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya mayar da nuna bacin ransa ga tsangwamar tare da rashin adalci da yace ana nuna ma makiyaya yan Fulani.
Shehin Malamin ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da gidan rediyon BBC Hausa, inda yace babu yadda za’a yi a raba makiyayi da dabbobinsa, ya kara da cewa duk gwamnan da yake son hana kiwo a cikin gari, toh lallai sai dai ya koma sahara da mulki.
KU KARANTA: Kungiyar tsagerun Neja Delta ‘Avengers’ ta lashi takobin cigaba da karya tattalin arzikin Najeriya
Dahiru Bauchi ya yi wannan batu ne duba da sabbin matakai na hana kiwo da wasu gwamnoni suka kirkiro a jihohinsu, wanda a ganinsu hakan ne zai kawo karshen rikita rikita tsakanin manoma da makiyaya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Malamin yana fadin cewa rashin adalcin da ake yi ma Fulani ne dalilin daya haifar da wannan rikici: “An siyar da burtalolin da makiyaya ke amfani dasu wajen kiwon dabbobi, kuma gwamnati na gani, babu abinda tayi game da haka.
“Gwamnatoci uku muke dasu, ta karamar hukuma, ta jiha da kuma ta tarayya, ita tarayya ta fi kowa hakki, amma idan matsalat bai shafe ta ba, toh ba ruwanta.”
Da aka tambayeshi bayan ganin lafin masu kiwon dake yawo dauke da bindigu? Sai shehin Malamin ya kada baki yace: “Mutum ba zai kare kansa ba?”
A yan kwanakin nan ana samu karuwar rikice rikice da kai hare hare tsakanin makiyaya da manoma, musamman a jihohin Taraba, Benuwe, Nassarawa da kuma jihar Kaduna.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng