Barazanar Kisa: Wani direban mota ya roƙi kotu ta raba aurensu da uwargidansa
Wani direban motar haya, Laisi Ajibade, ya roƙi wata kotun al'adu dake birnin Ado-Ekiti akan ta raba aurensu da uwargidansa, Folake 'yar shekaru 22, a sakamakon barazanar gutsure masa mazakuta.
Ajibade mai shekaru 48 a duniya, ya tuhumi Folake da cin amana da kuma ƙaurace masa daga dukkan zamantakewa ta aure.
Mazaunin na jihar Ekiti ya bayyana cewa, Folake tayi barazanar yanke masa mazakuta a ranar 7 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata a yayin da ya bukaci kusantuwa da ita.
Yake cewa, "tayi barazanar kashe ni a duk lokutan da muka samu sa'insa; Ina jin tsoron zama tare da ita karkashi rufin kwano daya".
KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta saki fursunoni 368 a jihar Kano
Legit.ng da sanadin jaridar The Punch ta fahimci cewa, wannan aure ya albarkatu da 'ya'ya hudu, inda Ajibade ya roƙin kotun aka ta raba auren dake tsakaninsu kuma ta ƙyale masa mallakin 'ya'yan.
A sakamakon rashin ƙwararan dalilai, alkaliyar kotun Misis Olayinka Akomolede, ta daga sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu domin ci gaba da shari'a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng