Hadimin shugaba Buhari ya bawa makiyaya shawara mai muhimmanci
- Mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu, ya bawa makiyaya shawarar yadda zasu zauna lafiya da kowa
- Ya jajantawa mutanen jihar Benuwe bisa asarar rayuka sakamakon rikicin makiyaya
- Shugaba Buhari ya ci alwashin hukunta duk masu hannu cikin kashe-kashe a jihar Benuwe
Mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu, ya yi kira ga makiyaya da su rungumi harkar kiwon zamani da kuma sabuwar fasahar kiwon dabbobi domin samun zaman lafiya tsakaninsu da manoma.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar, Ojudu, ya bayar da wannan shawara ne yau, a filin tashin jirgin sama na Murtala Muhammed dake jihar Legas.
Ojudu ya ce rungumar hanyar kiwo ta zamani za ta kawo zaman lafiya tsakanin makiyaya da manom, musamman a jihohin Benuwe, Taraba, da Nasarawa.
Hadimin na shugaban kasa ya jajantawa mutanen jihar Benuwe bisa asarar rayukan da aka samu sakamakon rigingimun makiyaya da manoma a jihar.
DUBA WANNAN: Wani shu'umin matsafi da ya kashe 'yan sanda biyu ya gamu da fushin sojojin Najeriya
"Shugaba Buhari ya damu kwarai da yawaitar kashe-kashen rayuka sakamakon rigingimu tsakanin makiyaya da manoma kuma zai hukunta duk masu hannu a cikin rikicin," inji Ojudu.
Ojudu ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin mutum mai kishin Najeriya da ba zai taba bari a cutar da kowacce kabila ba.
Ojudu ya bayyana cewar yana ziyarar al'ummar jihar Ekiti dake kasashen ketare domin yada manufar sa ta son tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben da za'a yi wannan shekarar.
Za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti a cikin shekarar nan da muke ciki. Tuni masu son yin takarar gwamnan jihar a jam'iyyu daban-daban suka fara yada manufofinsu ga masu zabe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng