Wani direban mota ya gurfana a gaban kuliya da laifin ɗauke matar maƙwabcinsa

Wani direban mota ya gurfana a gaban kuliya da laifin ɗauke matar maƙwabcinsa

Wani direban mota dan shekara 36, Emmanuel Peter, ya gurfana a gaban kuliya dake unguwar Karu a Abuja, wanda ake tuhumarsa da aikata laifin ɗauke matar makwabcinsa, Felicia Akpeku.

Wannan laifin da direban ya aikata ya sabawa sashe na 27 cikin dokar kasa kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Sai dai Emmanuel bai amince da laifin da kotu ke tuhumarsa da shi ba, inda alkali kotun, Mista Hassan Ishaq, ya bashi damar beli akan kudi naira dubu 100 tare da ta gabatar da mutum daya da zai tsaya masa a matsayin jingina ya kuma daga sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Fabrairu.

Mista Mahmud Isma'ila, jami'in dan sanda mai shigar da kara a gaban kotu ya bayyana cewa, mijin wannan mata, Akpeku Godewin, shine ya kai korafi ofishin 'yan san dake Nyanya tun a ranar 12 ga watanJanairu.

Wani direban mota ya gurfana a gaban kuliya da laifin ɗauke matar makwabcinsa
Wani direban mota ya gurfana a gaban kuliya da laifin ɗauke matar makwabcinsa

A cewar jami'in dan sandan, Mista Akpeku da mai dakinsa sun samu wata 'yar rashin jituwa ne tsakaninsu , inda tayi ƙaura zuwa gidan maƙwabcinsa Emmanuel.

KARANTA KUMA: Wani magidanci ya lakadawa uwargidansa duka har lahira a jihar Jigawa

Mai gabatar da ƙarar ya ci gaba da cewa, wanda ake tuhuma ya baiwa matar maƙwabcinsa masauki har zuwa wayewar gari tare da ba ta kudi domin ta kama gabanta.

Ya ƙara da cewa, mijin wannan mata yana roƙon kotu akan ta hukunta maƙwabcinsa da ya tallafawa mai dakinsa ta kama gabanta ba tare da izininsa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel