Kimanin 'yan Najeriya 1,400 hukumomi a kasar Sifen suka kubutar daga mutuwa
- Kimanin mutum 1,400 hukumomi a kasar Sifen suka kubutar daga mutuwa a teku
- Wasu mutum biyu sun mutu saboda tsananin galabaita
- Majalisar dinkin duniya (UN) ta ce kimanin 'yan ci-rani 173 ne suka mutu yayin tsallaka tekun tun shigowar shekarar nan
Wasu 'yan ci-rani kimanin 1,400 daga Najeriya sun auna arziki bayan da hukumomin kasar Sifen suka tserar da su daga mutuwa a tekun bahar maliya bayan da jirgin dake dauke da su ya kusa ya kife a daf da gabar tekun.
Wata kungiya, Spanish Charity Proactiva Open Arms, ta bayyana cewar ta kaiwa 'yan ci-ranin gudunmawa ne bayan sunyi lodin da ya wuce ka'ida a cikin wani jirgin ruwa. Kungiyar ta ce sun samu 'yan gudun hijirar cikin yanayi mai matukar hatsari, tare da bayyana cewar yaro daya ya mutu saboda tsananin galabaita.
DUBA WANNAN: 'Yan ci-rani 200 daga Najeriya da wasu kasashen Afrika sun dulmiye a teku
Jiragen ruwa mallakar kasar Italiya da kungiyar kasashen Turai (EU) sun ce sun kubutar da 'yan gudun hijirar ne daga wasu kananun jiragen ruwa masu karancin ingancin lafiya. Cikin jiragen dake dauke da 'yan ci-ranin har da na katako.
Daga cikin wadanda aka kubutar akwai mata 175 da kananan yara 75, dukkaninsu sun galabaita. Kazalika wasu mutum biyu, ciki harda karamin yaro, sun mutu.
Kimanin mutum 1,000 hukumomin kasashen turai suka kubutar ya zuwa kasar Italiya tun shigowar shekarar nan.
Wata kungiyar majalisar dinkin duniya mai kula da 'yan gudun hijira da ci-rani ta ce mutane 173 ne suka mutu a sabuwar shekarar nan da muke ciki yayin kokarin tsallaka tekun ya zuwa kasashen Turai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng