Hukumar SSS ta gayyaci wani mallamin addinin Krista ofishin ta akan sukar Buhari da yayi
- El-Buba ya ce ya ki amsa gayyatar da hukumar SSS suka mishi saboda sun saba kai'dar gayyata
- A makon da yagaba ta ne wani mallamin addinin Kritsa yayi kira ga yan Najriya kada su kuskura su kara zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari
Mallamin addinin Krista da yaki amincewa jami’an hukumar SSS su tafi da shi a lokacin da suke kama shi a Jos, yace yaki amsa gayyatar da hukumar SSS suka mishi saboda ya saba ka’ida.
Fasto, Isa El-Buba, ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da ya zanta da manema labaru a Jos.
Mr. El-Buba ya ce mataimakin daraektan hukumar SSS, sun kai wa cocin sa sammame a lokacin da yake shirin yin wa’azin tsakar dare, amma yaki amsa gayyatar da hukumar ta mishi saboda ba rubuce suka mishi gayyatar ba.
“Na tambaye su wasikar gayyata a lokacin da suka zo tafiya dani amma basu zo da shi ba," inji El-Buba.
KU KARANTA : Gwamnatin jihar Nassarawa tace zataci gaba da taimakawa 'yan gudun hijira
EL-Buba yace ya san bai yi wani laifi da ya tambaye su wasikar gayyata ba. Kuma ya ce ya dau alwashin cigaba da wa’azi akan gwamnati idan tayi kuskure duk da barazanar kama shi da ake yi.
A makon da ya gaba ta ne El-Buba ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari akan nuna halin ko’in kula da kashe-kashen da makiyaya suke yi a fadin kasar da kira ga al’umma Najeriya kada su kuskura su kara zaban shi a 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng