Wani magidanci ya lakadawa uwargidansa duka har lahira a jihar Jigawa
Hukumar 'yan sandan jihar Jigawa, ta cafke wani dattijo dan shekara 50 da yayi sanadiyar mutuwar uwargidansa mai shekaru 40 a karamar hukumar Birnin Kudu dake jihar Jigawa.
Kakakin hukumar, SP Jinjiri Abdu, shine ya tabbatar da faruwar hakan a ranar talatar da gabata, inda yace mutumin da ake zargi ya lakadawa uwargidansa duka ne bayan wata 'yar jayayya da shiga tsakaninsu da misalin karfe 6:30 na safiyar ranar 14 ga watan Janairu a gidansu na aure dake kauyen Daurawa.
Kididdigar bincike ta bayyana cewa, dawowar wannan maigida daga tafiya ke da wuya, sai ya garzaya gidan amaryarsa, inda a yayin da marigaya ta samu labari sai ta kwashi kafafu har gidan amarya domin nuna rashin amicewarta.
Rahotanni da sanadin SP Jinjiri sun bayyana cewa, kafin tafiyar wannan maigida, yana tare ne da marigayar wanda ya kamata ya kasance tare da amaryarsa bayan ya dawo daga tafiya.
KARANTA KUMA: Ka yi ƙarya kan kisan gillar da aka yiwa makiyaya a Taraba, CAN ta gaya wa Sanusi
A yayin haka ne amaryar ta yarjewa mijin nasu ya kasance da uwargidanta domin a zauna lafiya, inda marigaya da mijin suka ci gaba da jayayya da har ya fusata na yi mata jina-jina kuma ya mika ta asibiti.
An yi rashin sa'a wannan uwargida tace ga garinku nan tun kafin malaman asibiti su kawo gareta.
Jami'in dan sandan ya kara da cewa, tuni aka gudanar da jana'izar marigayiya, inda bincike zai ci gaba da gudana domin gurfanar wannan magidanci a gaban kuliya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng