Kashe Fulani 800 da sarki Sanusi ya ce anyi a jihar Taraba karya ce – Gwamnatin Taraba, CAN
- Gwamnatin jihar Taraba da Kungiyar CAN sun karyata sarki Sansui Lamido akan maganar da yayi na cewa an kashe Fulani 800
- Kungiyar CAN resehn jihar Taraba ta roki Sansui ya daina karya da yada farfaganda dan kare mutanen sa da kowa yasan su ke kashe-kashe a kasar
Gwamnatin jihar Taraba da kungiyar Kristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Taraba, sun karyata Sarkin Kano, Mai martaba, Muhammadu Sanusi II, akan maganar da yayi na cewa an kashe Fulani 800 a shekarar da ta gabata.
A wata hira da sarki Sanusi yayi, da Jaridar Sunday Punch, yace an kashe Fulani 800 a Mambila Filatu dake jihar Taraba a cikin wata karshen mako.
“Ni da kaina na aika wa gwamnatin tarayya hotuna da sunayen Fulani 800 da aka musu kisan gillar a Taraba tare da sunayen mutanen da suka aikata wannan laifin amma babu abun da aka yi,” inji Sanusi.
KU KARANTA : Gwamnatin jihar Nassarawa tace zataci gaba da taimakawa 'yan gudun hijira
Amma gwamnan jihar Taraba, ta kwamishinan sharia da babban lauyan jihar, Yusufu Akirikwen, ya ce maganar da sarki Sanusi yayi ba gaskiya bace.
Bayan haka a wata sanarwa da kungiyar Kristocin Najeriya (CAN) ta fitar ta mai magana da yawun bakin ta, Dr. Ben Ubeh, kungiyar ta karyata maganar da sarki Sanusi yayi, inda ta roki shi ya daina yada labarun karya da farfaganda dan kare mutanen sa da kowa yasan su kashe-kashe kusan kowani rana a fadin kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng