Dandalin Kannywood: Da cikkaken goyon bayan iyaye na na fara fim - Khadija Mustapha

Dandalin Kannywood: Da cikkaken goyon bayan iyaye na na fara fim - Khadija Mustapha

Sanannar jarumar nan ta wasannnin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Khadija Mustapha ta bayyana cewa ita da cikakken goyon baya da kuma masanaiyar iyayen ta ta fara harkar fim.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da wata mujallar fina-finan Hausa din a kwanan baya inda take bayar da ansa a kan tambayar da aka yi mata game da yadda akayi ta samu kanta a cikin harkar fim.

Dandalin Kannywood: Da cikkaken goyon bayan iyaye na na fara fim - Khadija Mustapha
Dandalin Kannywood: Da cikkaken goyon bayan iyaye na na fara fim - Khadija Mustapha

KU KARANTA: Bana sha'awar auren Buhari - Fati Shu'uma

Legit.ng ta samu cewa jarumar dai ta bayyana cewa ita gaskiya bata samu wani cikas ba mai yawa yayin da ta fara fitowa a fina-finan na Hausa kasantuwar sai da ta samu cikakken goyon bayan iyayen ta sannan ta fara.

Haka zalika jarumar ta kuma bayyana cewa tun tana karama take sha'awar fitowa a fim din amma sai da tayi aure ta fito sannan Allah ya cika mata burin ta.

Da take bayani game da aure, jarumar ta bayyana cewa a shirye take ta yi aure ko wane lokaci idan dai har Allah ya bata mijin da take so kuma yake son ta tsakani da Allah.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng