Zaman dar-dar a Plateau bayan da fulani suka sanar da sace masu shanu 350

Zaman dar-dar a Plateau bayan da fulani suka sanar da sace masu shanu 350

Ana cikin zaman dar-dar a jihar Plateau dake a arewacin kasar nan bayan da shugaban kungiyar fulani makiyaya na yankin suka bayar da sanarwar kashe masu dan uwa tare kuma da sace masu shanu fiye da 350 a karamar hukumar Riyom.

Haka nan ma dai kuma mun samu cewa Hankula sunyi matukar tashi a garin Jos, babban birnin jihar Plateau a jiya Talata bayan da wasu matasan da suka tasarwa 100 suka zagaye gidan wani babban malamin kirista a yankin inda kuma suka hana jami'an 'yan sandan farin kaya su kama shi.

Zaman dar-dar a Plateau bayan da fulani suka sanar da sace masu shanu 350
Zaman dar-dar a Plateau bayan da fulani suka sanar da sace masu shanu 350

KU KARANTA: Wasu ma'aurata sun makale suna jima'i

Kamar dai yadda muka samu daga majiyoyin mu, malamin mai suna Isa El-Buba dai shine shugaban rukunin coci-coci na Evangelical Outreach Ministries international a turance kuma an bayyana shi da mai yin wa'azi mai zafi game da caccakar gwamnati.

Legit.ng ta samu dai cewa sai dai jim kadan bayan da matasan unguwar suka samu labarin shigowar jami'an na 'yan sandan farin kaya, sai kawai suka zagaye gidan inda kuma suka samu nasarar hana kama malamin.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga rundunar 'yan sandan jihar Legas na nuni ne da cewa wani uba mai suna Edet Asuquo ya tsere ya bar gidan sa bayan da ya shararawa diyar sa mari mai kwanaki 21 kacal a duniya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng