Boko Haram tayi asarar manyan mayaka 2 a yayin artabun su da sojin Najeriya
Labari mai dadin da muke samu daga majiyar mu na nuni ne da cewa sojoji da kuma mafarauta sun samu nasarar kashe wasu manyan mayakan kungiyar nan ta Boko Haram dake ci gaba da yaki da jami'an tsaro a garin Madagali, jihar Adamawa.
Haka nan ma mun kuma samu cewa mayakan na Boko Haram sun samu nasarar kashe wasu mazauna garin na Madagali su 3 a yayin harin da suka kai masu a jiyan.
KU KARANTA: Na fasa auren Buhari - Fati Shu'uma
Legit.ng haka zalika ta samu cewa daya daga cikin mazauna garin da lamarin ya auku kan idon sa ya bayyana cewa 'yan Boko Haram din da suka far wa garin nasu sun yi ta barin wuta tare da kone-kone kafin daga bisani su kona asibitin garin na Madagali a daren ranar Litinin.
A wani labarin kuma, mun samu cewa Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Legas ta sanar da samun nasarar cafke wani shehin malamin Islama mai suna Abdulfatai Kayode da wasu sassan jikin dan adam a unguwar Alakuko.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng