Yan sanda sun kama wani kasurgumin 'mahaukacin' barawo a Legas
Wani kasurgumin barawo dake badda kama kamar ta mahaukaci mai suna Olayinka Ogundamiro ya shiga hannun jami'an tsaron rundunar 'yan sandan Najeriya na shiyyar jihar Legas bayan da dubin sa ta cika.
Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, Mista Ogundamiro mai shekaru 25 kacal a duniya ya shiga hannun 'yan sandan ne a ranar Litinin din da ta wuce tare da wata jikkar sa da aka samu wayoyin hannu masu tarin yawa.
KU KARANTA: Da da na ya yi shaye-shaye kwara ya mutu in ji shugaban NDLEA
Legit.ng ta samu har ila yau cewa sauran kwarankwacaman da aka samu a cikin jihar ta sa sun hada da katin karbar kudi a bakunna da dama, injin karbar kudi na baki, kwamfuta da kuma kunkuru mai rai duk dai a cikin jakar ta sa.
A wani labarin kuma, Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Legas ta sanar da samun nasarar cafke wani shehin malamin Islama mai suna Abdulfatai Kayode da wasu sassan jikin dan adam a unguwar Alakuko.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng