Mabiya akidar shi’a sun ƙirƙiro sabon salon yin mubaya’a ga Ibrahim El-Zakzaky

Mabiya akidar shi’a sun ƙirƙiro sabon salon yin mubaya’a ga Ibrahim El-Zakzaky

Wata sabuwa Inji yan caca, a nan ma wani sabon salon nuna kauna tare da nuna ana tare ga shugaban kungiyar yan shi’a na kasa Ibrahim Zakzaky ne mabiyansa suka kirkiro.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, kuma babban mawallafin labaru a yanar gizo, Jaafar Jaafar ne ya bayyana hakan a shafinsa, inda ya tuna baya a zamanin yana yaro.

KU KARANTA: Gwamnati ta yi rusau a gidan Uwargidar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Yan shia
Ibrahim El-Zakzaky

Wannan sabon salo kuwa shine yadda wasu yan shi’a suka tsiri sanyan makarin wuya, irin wanda shugabansu Ibrahim Zakzaky ya sanya a fitowarsa ta farko tun bayan da aka daure shi a shekarar 2015, inda ya gana da manema labaru.

Legit.ng ta ruwaito yadda mawallafin ke dangantan sabon salon yan shi’an ga addu’ar nan da ake yi do tsorata kananan yara idan suna kwaikwaiyan marasa lafiya ko kuma mahaukaci ‘Allah ya mai da koko masaki’.

Mabiya akidar shi’a sun ƙirƙiro sabon salon yin mubaya’a ga Ibrahim El-Zakzaky
Yan Shia

Daga karshe mawallafin ya nuna rashin dacewar yin hakan, musamman idan da gaske suke na ganin an sako musu jagoransu.

Mabiya akidar shi’a sun ƙirƙiro sabon salon yin mubaya’a ga Ibrahim El-Zakzaky
Yan shia

Idan za’a tuna a ranar asabar 13 ga watan Janairu ne dai hukumar tsaro ta sirri DSS ta baiwa Zakzaky damar ganawa da menema labaru,inda ya tabbatar ma duniya cewar lafiyanshi kalau, ba kamar yadda wasu ke yayatawa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng