Yanzu-yanzu: An damke malami da sassan jikin mutum
Jami'an yan sanda a yau Talata sun damke wani malami mai suna, Alfa Kayode Abdul-Fatai, a unguwar Alakuko jihar Legas da sassan jikin mutum har da farjin mace.
Malamin wanda aka kama a gidam mai lamba No. 4, Okedumola Street, Off Obadare da zuciya da cinyan mace.
Kakakin hukumar yan sanda jihar Legas, SP Chike Oti, ya ce an damke malamin ne bisa ga labarin da aka samu ta hanyar bincike.
Oti ya ce yayinda aka yi masa tambayoyi ya bayyana cewa wani abokinsa ne ya bashi sassan jikin kuma shi ma an kama shi.
KU KARANTA: Anyi girgizar kasar a birnin Madina
Kwamishanan yan sandan jihar, Edgal Imohimi, ya yi kira ga mutane sun san abinda makwabtansu ke yi kuma su kawo kara ga jami'an tsaro.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng