In baka yi, bani wuri: Shigar makiyaya wani ƙauye ya sanya kowa ya ranta ana-kare

In baka yi, bani wuri: Shigar makiyaya wani ƙauye ya sanya kowa ya ranta ana-kare

Sama da mutanen wani kauye su 300 ne suka yi ta kansu yayin da labarin shigar wasu makiyaya kauyen ya bazu, mai suna Amek Ibeku na karamar hukumar Umuahia ta Arewa, jihar Abia.

Daily Trust ta ruwaito da asubahim ranar Litinin ne makiyayan suka isa jihar tare da shanunsu, duk da kokarin da mutan kauyen suka yi na hana su shiga.

KU KARANTA: Yan majalisu sun wasa wukarsu don bincikar dala miliyan 44 da suka ‘ɓace’ a hukumar liken asiri

Rahotanni sun tabbatar makiyayan sun shigo ne daga makwbatan kauyen, kamar yadda dakacin kauyen, Cif Ochionye Chilaka ya shaida ma majiyar Legit.ng, wanda yace da isan makiyayan, sai suka fara harbin iska da bindigoginsu, hakan ya sanya jama’an kauyen tserewa cikin dazuka don tsira da rayukansu.

In baka yi, bani wuri: Shigar makiyaya wani ƙauye ya sanya kowa ya ranta ana-kare
Yan bindiga
Asali: Depositphotos

Dakaci yace: “Wasu yan uwana ne suka kira ni cewa makiyaya sun kawo mana hari, har ma sun fara banka ma gonakinmu wuta, don haka na aika da wakilai na su roke su kan su fita daga garin, sai suka yarda, amma daga karshe suka dawo da yawansu, dauke da muggan bindigu.”

Yayin da majiyar tamu taisa kauyen, ta tarar da an girke Sojoji dauke da makamai sun zagaye kauyen, don samar ma mutanen tsaro, haka zalila kwamishinan watsa labarum jihar, John Okiyi Kalu ya ziyarci kauyen, inda ya basu tabbacin gwamnatu zata biyasu asarar da suka yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel