Dubun wasu 'yan damfara dake amfani da lambobin wayar Ambode suna wawure kudin jihar Legas ta cika

Dubun wasu 'yan damfara dake amfani da lambobin wayar Ambode suna wawure kudin jihar Legas ta cika

- Gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da wasu damfara

- 'Yan damfaran na amfani da wani siddabarun zamani mai amfani da wayar hannu

- An kama su bayan sun nemi babban akawun jihar Legas ta tura masu miliyan 50

Gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da wasu kwararrun 'yan damfara guda biyu bayan sun yi amfani da wata hikima sun nemi babban akawun jihar Legas ta tura miliyan 50 zuwa asusun ajiyar daya daga cikinsu. 'Yan damfaran na kiran jami'an gwamnatin jihar da lambobin wayar hannu na gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode.

Dubun wasu 'yan damfara dake amfani da lambobin wayar Ambode suna wawure kudin jihar Legas ta cika
Gwamnan Jihar Legas Ambode
Asali: Twitter

An gurfanar da wadanda ake zargin, Rilwanu Jamiu da Balogun Oyewole, gaban mai shari'a, Sedoten Ogunsanya, na babbar kotun jihar Legas dake Igboser. Ana tuhumar su da laifukan da suka hada da mallakar wasu bayanan gwamnati ta barauniyar hanya, sojan gona, da kuma damfara.

DUBA WANNAN: 'Yan Najeriya 14 da aka yankewa hukuncin kisa a Madinah sun aiko wa da Buhari sako

Babbar akawun gwamnatin jihar Legas, Abimbola Shukurat Umar, ta shaidawa kotu cewar ta samu sako a wayar ta daga gwamnan jihar a ranar 10 ga watan Fabrairu, 2016, dake umartar ta biyan Naira miliyan 50 zuwa wani asusun ajiya dake bankin Keystone. Ta kara da cewar sakon wayar ya sabawa yadda gwamnati ke fitar da kudi daga asusun jihar, hakan ya saka ta jan hankalin gwamnan, wanda nan take ya musanta aika sakon tare da bayar da umarnin fara binciken tushen sakon.

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS) ce ta bankado wadanda suka aika sakon da sunan gwamna Ambode.

Bincike ya tabbatar da cewar daya daga cikin mutanen da aka gurfanar (Oyewole) darekta ne a wani kamfani, Clayder Limited, kuma asusunsa ne aka nemi a tura miliyan hamsin din.

Bayan sauraron shaidu da hujjojin gwamnati, kotu ta daga sauraron karar ya zuwa 14 ga watan Fabrairu domin cigaba da sauraron karar, kazalika kotun ta bayar da umarnin tsare wadanda ake tuhuma a gidan yari na kirikiri dake jihar Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng