'Yan takara 725 zasu fafata a zaben kananan hukumomin jihar Filato
Hukumar zabe reshen jihar Filato ta bayyana cewa, ta tantance 'yan takara 725 da zasu fafata a zaben kujerun ciyamomi da kansiloli na kananan hukumomin jihar da za a gudanar a ranar 17 ga watan Fabrairu.
A yau talata shugaban hukumar Mista Fabian Ntung, ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a birnin Jos.
Ntung yake cewa, akwai 'yan takarar ciyamomi 48 da suke hankoron kujeru a kananan hukumomi 17, sai kuma 'yan takara 677 da suke neman kujerun kansiloli a fadin jihar.
Shugaban ya bayyana fatan cewa, zabe mai gabatowa zai kasance cikin tsari da kuma adalci bisa la'akari da matakin shirye-shirye da ak ci gaba da gudanarwa.
KARANTA KUMA: Haihuwar 'ya'ya rututu ta salwantar da wani auren shekaru 9 a jihar Legas
Ya yaba da goyon baya tare da hadin gwiwa da jam'iyyu daban-daban suka bayar a jihar kuma ya bukaci su ci gaba har zuwa karshen zaben.
Ntung ya kuma bukaci jam'iyyun da su amintu da hukumar duba da irin dukufonta na yin shiri don gudanar da zaben da zai zamto mafi nagarta da inganci a tarihin jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng