Gwamna Tambuwal ya sanya farfesa ta farko a jihar Sakkwato cikin majalisar sa
A yau ne gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, ya rantsar da kwamishinoni hudu a jiharsa wadanda suka hadar da har da wata farfesa ta jami'ar Usman Danfodio. Farfesa Aishatu Madawaki ta kasance farfesa ta farko a duk fadin jihar.
Sauran kwamishinonin da gwamna Tambuwal ya rantsar sun hadar da; Ahmed Barade Wammako, Garba Yakubu Tsitse da kuma Bello Isa Ambarura.
A yayin haka dai, gwamnan ya kuma rantsar da tsohon dan majalisar wakilai, Umar Bature da kuma tsohon shugaban kwalejin ilimi ta jihar, Dakta Bello Rabi'u, a matsayin masu bashi shawara ta musamman da kuma Alhaji Bello Buba a matsayin shugaban karamar hukumar Wammako ta jihar.
Da yake jawabi a bikin da aka gudanar a fadarsa, Tambuwal ya yi kira ga sabbin wakilai don daukar ayyukansu a matsayin kira zuwa yiwa jihar hidima.
A jawabinsa, "an zabe ku ne bisa ga cancantar ku da kuma tarihin kwazon wajen yiwa jihar Sakkwato hidima. Kuna da kwarewa a sassa dabn-daban na ingatawa al'umma kuma jihar ta sanya idanu a kanku domin ganin irin gudunmuwar ta zaku bata.
KARANTA KUMA: Ka yi ƙarya kan kisan gillar da aka yiwa Fulani a Taraba, CAN ta gaya wa Sanusi
Da yake jawabi ga sabon shugaban karamar hukumar Wamakko da aka zaba, Tambuwal ya roƙe shi ya dauki nauyin kalubalen gwamnati tare da gaskiya da aminci.
Legit.ng ta fahimci cewa, taron ya kuma bayar da shaida ta rantsar da Hassan Maccido a matsayin sakatare na dindindin, yayin da kuma aka rantsar da Ahmad Bell Mailato, Ahmad Rufa'i Ibrahim da Muslim Adamu a matsayin daraktoci na wasu ma'aikatun gwamnatin jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng